Blogs » Languages » Fulfulde » Yadda Za A Karanta A Kuma Rubuta FULFULDE

Yadda Za A Karanta A Kuma Rubuta FULFULDE

 • Yadda Za A Karanta A Kuma Rubuta
  FULFULDE
  (How To Read and Write Fulfulde)
  Domin Fulani waɗanda sun riga sun iya karatu da rubutun Hausa
  2nd Edition November 2004 500 Copies

  Game da neman ƙarin bayyani a kan abubuwan da aka rubuta a nan,
  �ka rubuta zuwa ga:
  Acting Fulfulde Literacy Coordinator P.O. Box 953 Jos, Plateau State
  Ka tabbata ka haɗa da adireshinka domin za a iya aika maka amsa.
  \u2756 Littattafai cikin Fulfulde;

  \u2756 Ƙara samun wannan littafi game da yadda za a karanta a kuma rubuta Fulfulde;

  \u2756 Azuzuwan da ake koyar da Fulani yadda za su yi karatu da rubutu a Fulfulde; \u2756 Littattafan da suke amfani da harshen Fulfulde domin a koyar da wani harshe kamar Turanci ko Hausa;

  \u2756 Yadda za ka taimaka ka koyar da mutane a azuzuwan da suke taimakon Fulani su koyi karatu da rubutu a cikin Fulfulde;

  \u2756 Yadda za ka ƙara koyi karatu da kyau a cikin Fulfulde, har ma ka iya rubuta littattafai a cikin Fulfulde domin mutanenka;

  \u2756 Yadda za ka sa hannunka wajen kafa da ƙarfafa aikin koyon karatu a cikin Fulfulde ko'ina a Nijeriya;

  KADA KA JI TSORO!
  Idan ka Bafulatani ne wanda ya iya Fulfulde sosai kuma ya riga ya iya karatu da rubutu cikin Hausa, karatu da rubutu a Fulfulde ba zai yi maka wuyan koya ba.


  A cikin Fulfulde akwai baƙaƙƙen da suna nan daidai kamar na Hausa:


  1. Waɗannan baƙaƙƙe daga baƙaƙƙen Hausa suna nan cikin baƙaƙƙen Fulfulde.  Ana faɗinsu da kuma rubuta su a cikin Fulfulɗe daidai kamar yadda ake faɗinsu da kuma rubuta su a cikin Hausa.


  a  b  ɓ  c  d  ɗ  e  f  g  h  i  j  k  l  m  n  o  p  r  s  t  u  w  y  '


  Duba yawan abin da ka riga ka sani game da karatu da rubutu a cikin Fulfulde!
  Kamar Hausa, Fulfulde ita ma tana da baƙaƙƙe masu lanƙwasa ɓ da ɗ.
  A cikin waɗansu tsofoffin littattafai za ka iya gani an rubuta baƙaƙƙe masu ƙananan lanƙwasa (ɓ da ɗ) kamar haka 'b da 'd.


  Misali:   'biraa'dam (madara) 'da'b'butuki (nema) Amma sa'ad da kake rubuta su, kullum ka rubuta su kamar haka: ɓ da ɗ.
  Misali:  ɓiraaɗam  (madara) ɗaɓɓutuki  (nema)


  2. Daidai kamar Hausa, akwai waɗansu baƙaƙƙe cikin Fulfulde waɗanda suke a ɗaure tare. Dubi misalan da aka rubuta a ƙasa. Faɗa kalmomin da suke da baƙaƙƙe a ɗaure a cikin Fulfulde, ka ga yadda kasancewarsu kawai yake canza ma'anar kalmomi.
  Misali:

  1.  O wuji nebbam  (Ta shafa mai.) O wujji nebbam  (Ta sata mai.)
  2.  Suka wuli.   (Yaro ya ƙone.) Suka wulli.   (Yaro ya yi ihu.)

  3.  Ɗum fuɗi booɗɗum!  (Ya tsira da kyau!) Ɗum fuɗɗi booɗɗum!  

           (Ya fara da kyau!)
  4.  Inna tami.    (Mama ta dunƙula shi curi-curi.) Inna tammi.  (Mama ta yi tsammani.)


  Sa'ad da ka ji baƙaƙƙen da suke a ɗaure, kowane lokaci ka rubuta wannan baƙin sau biyu. Kuma, sa'ad da ka ga an rubuta wani baƙi sau biyu kuma babu wani abu tsakaninsu, sai ka ɗaura muryarsu.


  Sa'ad da ba ka ji baƙaƙƙen da suke a ɗaure ba, sai ka rubuta baƙin nan sau ɗaya kawai. Kuma, sa'ad da ka ga an rubuta ɗaya na wani baƙi, kada ka fitar da muryarsa kamar baƙaƙƙe biyun da suke a ɗaure.


  A. Rubuta waɗannan kalmomi a cikin Fulfulde:
  Lura da kyau domin ka saurari dukan baƙaƙƙen da suke a ɗaure, ka kuma rubuta su daidai. (Amsoshinsu suna a ƙarshen wannan ɗan littafi.)
  1. Tafi!
  2. Zai ba ka wuya.
  3. Ba matan nan koryan.
  4. Saniyarmu tana a ɗaure a daji.
  5.  Kunu ta lalace.
  Waɗansu abubuwa a cikin Fulfulde sukan bambanta da na Hausa:
  1. Muryar baƙin nan "c" a cikin Fulfulde.
  Ana yin amfani da baƙin nan "c" a cikin Fulfulde domin muryar "c" da muryar "sh" na cikin Hausa.

   

  Misali: Ga wata kalmar da ake amfani da ita a cikin Fulfulde da Hausa: HAUSA:   shawara FULFULDE:    caawari
  Muryar da take gaban waɗannan kalmomi biyu murya ɗaya ne.   A cikin Hausa ana rubuta muryar da "sh"; a cikin Fulfulde ana rubuta muryar da "c".


  2. Yanzu haka ana amfani da baƙin nan "w" a cikin Fulfulde a kan muryoyi biyu.
  A cikin Fulfulde na mutane da yawa, akwai iri biyu na baƙin nan "w".


  Misali: Ka faɗi jam'i biyun nan da aka rubuta cikin Fulfulde:


  1. Suka gaɗɗiiɗo mbabba ngan, haani o wurto o jooɗo booɗɗum.
  (Yaron da yake a zaune a kan jakin can, dole yã miƙe kansa yă zauna da kyau.)
  2. Suka mo nder suudu ndun, haani o wurto o jooɗo e yaasi.
  (Yaron da yake cikin bukkar can, dole yă fita yă zauna a waje.)
  Ko ka iya ji cewa muryar "w" a cikin "wurto" ta biyu ta bambanta da muryar "wurto" ta farkon?
  Domin a bambanta muryoyi guda biyun nan, waɗansu mutane sukan rubuta irin "w" na biyun da baƙi "v". Wannan ba ya nufi cewa ana faɗinsa kamar "v" na cikin Turanci; hanya ce kawai na bambanta baƙaƙƙe biyu, wato bambancin muryoyi biyu, cikin Fulfulde.
  Ga yadda za mu rubuta jam'i na biyu wanda aka rubuta a bisa muna amfani da "v".
  Suka mo nder suudu ndun, haani o vurto o jooɗo e yaasi.
  (Yaron da yake cikin bukkar can, dole yă fita yă zauna a waje.)
  Amma a wannan lokaci hanyar rubutun Fulfulde tana rubuta dukan muryoyin nan da baƙin nan "w".

  3. A cikin Fulfulde wasulan da ake ja, ana rubuta su dabam da yadda suke a cikin Hausa.
  A cikin Hausa wasulan da ake ja ana rubuta su kamar haka: â   ç î ô û Amma a cikin Fulfulde wasulan da ake ja ana rubuta su kamar haka: aa ee ii oo uu
  Wasulan da ake ja suna da murya dabam kuma dole ne a rubuta su dabam-dabam.
  Sa'ad da ka ji an ja wasali, dole ne ka rubuta wasalin sau biyu.
  Kuma, sa'ad da ka ga an rubuta wasalin sau biyu ba tare da wani abu tsakaninsu ba, sai ka ja wannan wasalin: Misali:   O huuli caangol. (Ya haye rafi.) Sa'ad da ka ji ba a ja wasalin ba, dole ne ka rubuta wasalin sau ɗaya kawai.  Kuma, sa'ad da ka ga wasali guda ɗaya yana nan shi kaɗai, KADA ka ja wannan wasalin.
  Misali:   O huli laahooru.      (Ya ji tsoron kare.) Wasula biyar nan ne kaɗai za a iya ja.
  \u2756 Fulfulde yana kuma da wasula da yawa waɗandan ake ja a ƙarshen kalmomi.
  Idan babu wata kalma biye da kalmar da ta ƙâre da wasalin da ake ja, za a iya FAƊIN wannan wasali kamar babu jan wasali a ciki.  AMMA dole ne a RUBUTA ta da wannan wasalin da ake ja.
  Idan kana rubuta kalma tare da wasali a ƙarshenta kuma kana so ka tabbata ko ana janta ko babu, sai kawai ka faɗi wannan kalma a cikin jam'in da take da wata kalma biye da ita.
  Sa'ad da ka yi magana da Fulfulde "Babu abin da zai ci." ko "Babu abin da ba zai ci ba.", wasalin da yake a ƙarshen jam'in ana iya FAƊINSA a hanya ɗaya:
  Walaa ko o nyaamata.
  Sa'ad da ka karanta wannan, yaya za ka yi ka bambanta ko ma'anar jam'i tana nufi "Babu abin da zai ci." ko "Babu abin da ba zai ci ba."?

  Yana da muhummanci muna da wata hanya ta bambanta a cikin rubutu waɗannan ma'anoni biyu na jam'in nan.  Shi ya sa dole ne mu tabbata mun rubuta dukan wasulan da ake ja duk inda suka kasance.
  Domin a gane wane "nyaamata" yana da wani wasalin da ake ja a ƙarshe, a sa wata kalmar da take da ma'ana a ƙarshen wannan kalmar.
  Kamar haka:
  Walaa ko o nyaamata e wuro.
  Yanzu idan ba a ja wasalin da yake a ƙarshen kalmar "nyaamata" ba, to mene ne ma'anar?
  Walaa ko o nyaamata e wuro.
  Ma'anar ita ce: "Babu abin da zai ci (a gida)."
  Idan ana jan wasalin da yake a ƙarshen kalmar, to mene ne ma'anar?
  Walaa ko o nyaamataa e wuro.
  Ma'anar ita ce: "Babu abin da ba zai ci ba (a gida)."
  B. Rubuta waɗannan kalmomi da jimla a cikin Fulfulde: Ka lura da kyau ka saurari inda ake jan wasali ka rubuta wannan wasalin sau biyu.  Idan ba jan wasalin ba, sai ka rubuta wasalin sau ɗaya kawai. 

  (Amsoshinsu suna a ƙarshen wannan ɗan littafi.)

  1.  ɗaki

  2.  gado

  3.  jiri

  4.  tumaki

  5.  taurari

  6.  Ban san inda yake ba.

  7.  Sa'ad da ya zauna, wani yaro ya yi dariya.

  8.  Ba za ka yarda ba?

  9.  Babu abin da zai gani.
  10. Babu abin da ba zai gani ba.

   

  Ga waɗansu kalmomi na musamman waɗanda suke da wasulan da ake ja da waɗanda ba a ja domin ka tuna yadda za ka rubuta su:
  KALMA MISALI
  ko
  koo
  1.  Ko o waɗata?     (Me ya yi?)


  2.  Ko'o haako, a yiɗi mi unako, koo mi ɗalako?


  (Waɗannan ganye, kana so in daka su ko kuwa in bar su yadda suke?)


  3.  Koo ɗume ko o waɗi ɗum wooɗi, koo?
  (Komen da ya yi yana da kyau, ko ba haka ba?)
  To
  to'
  too       1.  Raa wuro to Hassan waali.
              (Wannan shi ne gidan da Hassan ya kwana.)
  2.          To Sule nanii habaru, o yahay wuro Reebo.
               (Idan Sule ya ji labarin, zai tafi gidan Reebo.)
  3.  To wuro maako woni?     (Ina ne gidansa?)


  1.  To' o yaha wuro gorko on.
  (Kada yă tafi gidan wancan mutum.)
  2.  Taa yahu wuro gorko on.
  (Kada ka tafi gidan wancan mutum.)
  Too, mi nani.  (To, na ji.)


  Maa
  ma
  Sukaaɓe maa e fija.           (Yaranka suna wasa.)
  Sukaaɓe Ali ma e fija.     (Yaran Ali su ma suna wasa.)


  Bo
  boo
  Ali metiri bo kaaɗo.
  (Ali yana magana kamar shi ba Bafulatani ba ne.)
  Abdu boo metiri bo Pullo!
  (Amma Abdu kuwa yana magana kamar Bafulatani.)


  Na naa
  Na mi wartii.      (Sai na dawo.)
  Naa o Pullo; o kaaɗo.
  (Shi ba Fulani ba ne, ba kuwa Bafulatani ba.)

   

  4. Fulfulde suna da waɗansu baƙaƙƙen da ake faɗinsu "ta hanci".
  Faɗi waɗannan jam'i biyu cikin Fulfulde:
  Nagge am wuudake.      (Saniyata ta kwanta ta ƙi ta tashi). Sukayel wuundake inna.      (Yaron ya rungumi mama.)
  Sâke faɗin kalmomin nan. Ka iya jin bambanci tsakanin kalmar Fulfulde wadda take da ma'ana "ta kwanta ta ƙi ta tashi" da kalmar Fulfulde wadda take da ma'ana "rungume"?
  Ana yin muryar "d" cikin "wuundake"  ta hanci, amma ba a yin muryar "d" cikin "wuudake" ta hanci. Sāke faɗi waɗannan kalmomi biyu cikin Fulfulde kana sauraron bambancin muryar "d" bayan sashi na "wuu" cikin kalmar. Kana iya jin bambancin?
  wuudake wuundake
  Yanzu faɗi kalmomin nan a Fulfulde:
  O     dilli.  (Ya tafi.) Ɓe  ndilli.  (Sun tafi.)
  Kana iya ji yadda murya tana fitowa ta hanci? Muryar "d" a cikin Fulfulde na "sun tafi" ita ce muryar "d" ta hanci.
  dilli ndilli
  Saboda muryoyin waɗannan baƙaƙƙe suna nan dabam-dabam, dole ne mu rubuta su dabam-dabam.
  Cikin Fulfulde akwai baƙaƙƙe guda huɗu waɗanda ake faɗinsu "ta hanci".  Su ne b, d, g, da j.
  Sa'ad suna cikin hanci, akan rubuta waɗannan baƙaƙƙe kamar haka:
  b ta hanci  mb   mbabba (jaki) d ta hanci  nd  nduungu (damina) g ta hanci  ng   ngaari  (bijimi) j ta hanci  nj   njayri  (wuri)


  C. Rubuta waɗannan kalmomi da jimla a cikin Fulfulde: Ka tabbata ka saurari kalmomin Fulfulde da kyau, ka kuma rubuta baƙaƙƙen da suke "ta hanci" daidai.  (Amsoshinsu suna a ƙarshen wannan ɗan littafi.)
  1. Akwai ruwa a cikin rijiya.
  2.  Ta rufe ƙwarya domin kada akuya ta sha madara.
  3. Wace saniya ce suka kama?
  4. Yau rana ta yi yawa! Shanu sun sha ruwa da yawa.
  5.  Na sayi farin ƙasa.
  5. Waɗansu baƙaƙƙen da ake faɗi ta hanci
  Faɗi kalmomin Hausan nan da aka rubuta a cikin harshenka na Fulfulde.  Yanzu ka maimaita su cikin Fulfulde kana kuma sauraron murya ta farkon kowace kalma.  Ka sāke maimaita waɗannan kalmomi uku cikin Fulfulde kana kuma saurari bambancin murya ta farko ta kowace kalma.  Kana iya ji yadda murya ta farko ta kowace kalma ta bambanta da sauran?
  Shiga.
  Ci.
  Ciza.
  Saboda muryarsu ta bambanta, ana rubuta su dabam-dabam. Ga yadda ake rubuta waɗannan muryoyi a cikin Fulfulde:
  n --  nattu  (shiga) ny --  nyaamu (ci) ŋ --  ŋatu  (ciza)
  6. Fulfulde yana da "y" na biyu wanda ake ce da shi "y da take da ƙaramar lanƙawasa ta sanda"
  Faɗi waɗannan kalmomin Hausa cikin Fulfulde.
  Ya sha.   [O yari.] Ya yi zane.  [O ƴari.]

  Yanzu ka sāke faɗinsu cikin Fulfulde kana sauraron murya a farkon kowace kalma.  Murya ta farkon kalma ce kaɗai take ba da bambancin ma'ana, ko ba haka ba?
  Sāke faɗi waɗannan kalmomi cikin Fulfulde kana sauraron bambancin murya ta farko ta kowace kalma. Kana iya jin yadda muryoyin farko suke bambanta da junansu?
  Saboda muryarsu ta bambanta, ana rubuta su dabam-dabam.  Ga yadda ake rubuta waɗannan muryoyi a cikin Fulfulde:
  y -- O yari.  (Ya sha.) ƴ -- O ƴari.  (Ya yi zane.)
  Sa'ad da kake rubuta wannan "y" mai ƙaramar lanƙwasa ta sanda, ka dinga fara da ƙaramar lanƙwasa ta sanda.
  Idan ka fara da wancan sashi na baƙin, ba za ka manta ka rubuta baƙin daidai ba.  Idan ka haɗa shi kamar 'yar wutsiya a kan "y", ba wuya ka manta ka haɗa shi.  Sa'an nan kalmar da kake so ka rubuta, ba ita ɗin ne ka rubuta ba.
  Duk lokacin da kake rubuta ɗaya daga cikin baƙaƙƙe masu ƙaramar lanƙwasa ta sanda (FULFULDE: "ɓaleeri ngoodundi cabel leliingel") -- wato ɓ, Ɓ, ɗ, Ɗ, ƴ, Ƴ -- kullum ka fara da ƙaramar lanƙwasa ta sanda.  Ta haka kullum za ka rubuta shi daidai.
  D. Rubuta waɗannan kalmomi da jimla a cikin Fulfulde: Ka saurari inda za ka rubuta baƙaƙƙen nan n, ny da ŋ.  Sa'ada da kake rubuta baƙaƙƙe masu ƙaramar lanƙwasa ta sawru, tuna ka fara da ƙaramar lanƙwasa ta sanda ɗin.  (Amsoshinsu suna a ƙarshen wannan ɗan littafi.)
  1.  jiki
  2. 'ya'yansu
  3.  Ka yi hamma.
  4.  Kuɗan zuma sun harbe su.
  5. Bushiya ta shiga ɗaki.

  6. Mun yini da masu kiwo.

  7. Dukansu haƙoransu suna yin musu zafi.

  8.  Ya hau.

  9. Malamai biyu suka zo.
  10. Sun kai masa bijimi, suka sha kendirmo, sa'an nan suka tafi.


  7. Ana rubuta wasula masu sākewa cikin Fulfulde a hanyar da ta yi dabam da ta Hausa.
  Saurari bambancin da yake cikin muryoyin kalmomi biyun nan.
  Murya ta tsakiyar kalmomin ita ce ta bambanta su, ko ba haka ba?
  paɗo  (takalmi) payɗo   (mutum mai ƙiba)
  A cikin kalmar nan "payɗo" kana iya ji yadda wasali (sashi na tsakiya) ya fara da muryar "a", sa'an nan ya zama muryar "y" a ƙarshe?  A cikin kalmar nan "paɗo" wasalin ba ta sākewa, murya ce kawai ta "a".
  A cikin Fulfulde, waɗansu wasula suna iya sākewa zuwa "y" a ƙarshe, waɗansu kuma suna sākewa zuwa "w" a ƙarshe.  Ga jerinsu da kuma yadda za a rubuta su:
  Masu sākewa zuwa "y" su ne: ay –  payɗo  (mutum mai ƙiba) ey –  leydi  (ƙasa) oy –  koyɗum (sauƙi) uy – wuyɓe  (ɓarayi)
  Masu sākewa zuwa "w" su ne: aw – jawdi  (dabbobi) ew – lewru  (wata) iw –  siwtaare (hutu) ow – dow  (sama)

  Sauranlittafi na nan da hausa (Download) The rest of the book.